Tattaunawa Da Ra'ayin Masu Saurare

Ra'ayoyin Masu Sauraro kan janye yajin aikin Likitoci masu neman ƙwarewa a Najeriya

Informações:

Synopsis

Shirin Ra'ayoyin Mai Sauraro na wannan Litinin tare da Nasiru Sani ya tattauna ne kan janye yajin aikin gargaɗi na kwanaki biyar da ƙugiyar likitoci masu neman ƙwarewa a Najeriya ta sanar a ƙarshen mako, kwanaki bayan fara ta a ranar Juma'ar da ta gabata, inda ta ƙara wa'aɗin makwanni  biyu don a biya musu buƙatunsu. Daga cikin buƙatun ƙungiyar da take nema gwamnati ta biya akwai abinda ya shafi albashi da alawus-alawus da kuma walwalar mambobinta. Ku latsa alamar sauti domin sauraron ra'ayoyin wasu daga cikin masu sauraro da suka aikoma ta manhajarmu ta Whatsapp