Synopsis
Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Alumma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalinariziki, aladu da dai sauransu
Episodes
-
Ra'ayoyin masu saurare kan karrama 'yan wasan Super Falcons da Tinubu yayi
29/07/2025 Duration: 10minTarihi dai ya maimaita kansa, inda tawagar Super Falcons ta Najeriya ta lashe gasar WAFCON karo na 10, bajintar da ba tawagar da ta taɓa yi. Sakamakon haka ne shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karrama ƴan wasan da lambar girmamawa ta ƙasa OON, da dala dubu dari-dari ($100,000) kowacce, da kuma gidaje a Abuja. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...
-
Ra'ayoyin masu saurare kan bikin cika shekaru biyu da juyin mulkin Nijar
28/07/2025 Duration: 10minA ranar Asabar da ta gabata, 26 ga watan Yuli Jamhuriyar Nijar ta yi bikin cika shekaru biyu a kasancewa a ƙarƙashin mulkin soji, wadanda suka hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum kuma suke cigaba da tsare shi ba tare da gurfanar da shi ba. A waje daya kuma a karon farko a jawabin da ya gabatar jagoran gwamnatin sojin Janar Abdourahmane Tchiani ya ce ya san halin ƙunci da jama’a ke ciki. Latsa alamar sauti domin sauraren ra'ayoyi mabanbanta...
-
Yau take ranar jin ra'ayoyin ku masu saurare kan batutuwa mabanbanta
25/07/2025 Duration: 09minA duk ranar Juma'a, RFI Hausa na bai wa jama'a damar tofa albarkacin bakinsu kan abubuwan da ke ci musu tuwo a ƙwarya kama daga siyasa, tattalin arziki, zamantakewa, harkokin yau da kullum da dai saurarensu. Latsa alamar sauti domin sauraren ra'ayoyi mabanbanta...
-
Ra'ayoyin masu saurare kan rahoton NBS na ƙaruwar tattalin arziƙin Najeriya
23/07/2025 Duration: 09minHukumar ƙididdiga ta Najeriya ta ce tattalin arzikin ƙasar ya samu ƙarin tagomashi da kashi 3 da ɗigo 13 a rubu’in farko na wannan shekarar ta 2025, saɓanin kashi 2 da ɗigo 27 yake a daidai wannan lokaci a shekarar 2024. Wannan na zuwa ne yayin da talauci ke ci gaba da ta’azzara a tsakanin al’ummar ƙasar, kuma manoma sun gaza yin noma yadda ya kamata saboda matsalar ta’addanci. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin...